Dussar ƙanƙara ta hana tashin jiragen sama
December 21, 2010
Kwanaki kaɗan kamin sallar Krismeti, dubun- dubunan matafiya sun maƙƙalle a filayen saukar jiragen sama daban-daban na nahiyar Turai, dalili da dussar ƙanƙara gami da sanhin hunturu da ke ci gaba da zuba. Filayen saukar jiragen sama na Frankfort, Landan, Paris, Amsterdam da Brussels, sun taƙaita zirga-zirgar.
A jiya sai da ma aka rufe wasu filayen saukar jiragen samar kwata-kwata har tsawan wani ɗan lokaci domin kwasar dussar ƙanƙara da ta taru.
A yanzu, da dama daga fasenjojin sun yin cincirido wajen jiragen ƙasa, wanda su ma ke fuskantar matasalar tushewar hanyoyin.Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa na Euro Star ta sanar da matafiyan cewar, babu sauran wuri cikin jiragenta, daga nan zuwa 24 ga wata.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal