Dussar ƙanƙara a Jamus | Labarai | DW | 30.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dussar ƙanƙara a Jamus

An soke tashin jirage a filin saukar jiragen sama na Francfort saboda zubar dussar ƙanƙara

Hukumomin kula da al ´amuran sufiri na jiragen sama sun soke tashi jirage sama 200 a filin saukar jiragen sama na birnin Francfort dake a yammacin Jamus.

Hukumomin sun ɗauki wannan mataki saboda rashin kyawan yanayin da ake cikinsa na dussar ƙanƙara da ke zuba kai a kai a Jamus

Wani kakakin hukumar filin jiragen saman  ya ce za a samu jinkiri ko a nan gaba, wajan tashin jiragen, saboda aikin da ake cikinsa na kakkaɓɓe dussar ƙanƙara da ta kwanta akan jiragen.

Mawallafi: Abdurahan Hassane

Edita: Yahouza Sadissou Madobi