Dumamar yanayi na barazana ga Duniya | Labarai | DW | 17.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dumamar yanayi na barazana ga Duniya

A wani lokaci a yau ƙwararrun masanannan na Majalisar ɗinkin duniya za su gabatar da rahoto, a game da gurbatar muhalli a duniya.Rahoton da za a gabatar a Valencia na ƙasar Spain, ana sa ran zai zama jagora ga sauran ƙasashen duniya wajen shawo kann matsalar ɗumamar yanayi a Duniya.Matsalar dumamar yanayi dai nada nasaba ne da yadda masana´antu da kuma Kamfaninnika ke fitar da gurbatacciyar Iskane.Bayanai sun nunar da cewa rahoton ana kuma sa ran zai kasance wani daftari ne da zai taimaka, wajen shawo kann matsalar ɗumamar yanayin, wacce a yanzu ke barazana ga Duniya.