Dukkan wakilan Hisbollah dake cikin gwamantin Libanon sun yi murabus | Labarai | DW | 11.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dukkan wakilan Hisbollah dake cikin gwamantin Libanon sun yi murabus

Bayan rushewar tattaunawar da aka shafe mako guda ana yi da nufin rage hauhawar tsamari a cikin gwamnatin Libanon, ministoci biyar ´yan shi´a na kungiyar Hisbollah da kawarta jam´iyar Amal sun yi murabus. Ministocin su 5 su ne wakilan Hisbollah a cikin majalisar zartaswar FM Fuad Libanon mai membobi 24. Murabus din na su ya kara jefa yanayin siyasar kasar ta Libanon cikin rudami. Duk da cewa ba zai kifar da gwamnati kai tsaye ba amma wannan mataki da ministocin suka dauka zai rage goyon bayan siyasa da gwamnati ke samu daga bangaren ´yan shi´a masu rinjaye kana kuma ya na iya sa kasar ta zama mai wuyar mulki ga FM Siniora wanda kasashen yamma ko marawa baya. Hisbollah dai na neman karin iko ne a cikin gwamnatin.