Dukkan mutane 113 dake cikin jirgin saman fasinjan Armenia da ya yi hadari sun mutu | Labarai | DW | 03.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dukkan mutane 113 dake cikin jirgin saman fasinjan Armenia da ya yi hadari sun mutu

Wani jirgin saman fasinja na kasar Armenia dauke da mutane 113 yayi hadari a cikin tekun Bahar Aswad dake kasar Rasha inda ya halaka dukkan mutanen da ke cikin sa. Ko da yake jami´an jirgin saman na Armenia sun ce rashin kyaun yanayi hade da hadari mai karfin gaske suka janyo faduwar jirgin, amma Sergei Kubinov shugaban sashen kudu na ma´aikatar kula da taimakon gaggawa ta Rasha ya ce shekarun jirgin da wasu dalilai na injuna ka iya haddasa hadarin. Masu binciken musabbabin faduwar jirgin saman sun ce ba wani aiki na ´yan ta´adda a ciki. A cikin shekara ta 1995 aka kera jirgin saman samfurin Airbus A-320, kuma an yi masa cikakken gyara a bara.