1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon ministan tsaron Jamus ya musanta yin rufa rufa a batun harin Kundus

November 28, 2009

Tsohon ministan tsaron ƙasar Jamus ya musanta yin rufa rufa a batun harin Kundus

https://p.dw.com/p/Kk2d
Tsohon ministan tsaro Franz Josef JungHoto: AP

Tsohon ministan tsaron ƙasar Jamus Josef Jung, tun da farko ma yana sane da abin da za iya biyo baya, bisa boye maganar mutuwar fararen hula a Afghanistan, bayan wani Kwamondan ƙasar ya bada umarnin kai hari a kan wata tankar maye.

'Yan mintoci kaɗan bayan miƙa takardar murabus ɗinsa, tsohon ministan tsaro, kuma wanda ya riƙe muƙamin ministan ƙwadago na 'yan kwanaki, bayan ta fito a fili ya yi ƙumbiya ƙumbiya bisa kisan fararen hula a ranar huɗu ga watan Satumba na wannan shekara, da akayi a lardin Kundus. Jung ya ce shi dama bai yi wata rufa rufa ba.

Na faɗawa al'umma da ma majalisar dokoki, bisa dukkan abin da na sani a wancan lokacin, kuma na bayyana musu komai, kai har yanzu ma ina shirye na bada ƙarin bayani

A wannan satin ne dai wata jarida a ƙasar ta Jamus, ta bankaɗo cewa, ma'aikatar tsaron ƙasar tana sane kuma ta boye wassu bayanai, waɗanda majiyar ƙungiyar tsaron NATO ta bayar, na cewa harin ya rutsa da fararen hula, waɗanda basu ji basu gani ba. Sabon ministan tsaron ƙasar Jamus Karl-Theodo zu Guttenberg, bayyi wata-wata ba sai ya sallami wani janar ɗin sojin ƙasar dama wani babban sakatare a hukumar tsaron ƙasar, biyo bayan abun kunya da ya faru. Duk da cewa shi kansa sabo ne a hukumar kuma har yanzu yana kan nazarin rahoton, kamar yadda yace.

Waɗan nan rahotonni da suke sabbi a gareni, ba yanzu ba ne zan iya bada amsar su, don haka ya kamata a bani lokaci, na karanta rahoton, shin menene ya faru, kuma wannan ba ƙaramin abu bane

Su dai 'yan adawa suna son kafa wani komitin bincike, haka ita ma gwamnatin ƙasar tana ganin akwai yawo da hankili a harkar sirrin sojin ƙasar. Don haka suke son kafa wani ɗan komiti a majalisar dokokin ƙasar, wanda zai gana cikin sirri, domin suna ganin akwai sauran batu da ke ɓoye. Inji wani masani kan harkar tsaro daga jam'iyar adawa ta The Green, Omid Nouripour.

Muna so mu sani ainihin rahotonni nawa ne, kuma me ya ƙumsa. Muna so muga dukkan rahotonnin, muna son sanin da yaushe ne, da wane lokaci ne rohoton ya zo, kuma wane minista ne ke da alhaki

Yayin da bincike ke ci gaba da gudana, ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta miƙa sunan wanda za ta maye gurbin muƙamin minista a ma'aikatar ta ƙwadugo.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Hauwa Abubakar Ajeje