Dubban mutane za su fiskanci yunwa a Najeriya | Labarai | DW | 08.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban mutane za su fiskanci yunwa a Najeriya

A cewar cibiyar ta MDD yara na mutuwa sannan akwai kimanin rabin miliyan da ke fiskantar barazana ta mutuwa muddin ba a kai musu agaji na abinci ba.

Fiye da mutane 120,000 za su fiskanci yanayi mai muni na karancin abinci a Najeriya dalilan da suka samu kansu a ciki ta silar aiyukan 'yan Boko Haram, wannan adadi ya kasance wani bangare na mutane kimanin miliyan 11 da su ke tunkarar matsalar ta karancin abinci a wannan shekara kamar yadda sabon rahoton MDD ya nunar.

A cewar hukumar abinci ta duniya FAO al'umma za su kasance cikin yanayi na bukatar abincin sosai tsakanin watannin Yuni zuwa Agusta a Arewa maso Gabashin kasar ta Najeriya.

Hukumar ta kara da cewa inda lamarin zai fi kamari shi ne jihar Borno mahauifar Boko Haram, wacce ita za ta sami kimanin kashi 65 cikin dari na al'ummar da za su sha fama da matsalar ta karancin abincin. A cewar cibiyar ta MDD yara na mutuwa sannan akwai kimanin rabin miliyan da ke fiskantar barazana ta mutuwa muddin ba a kai musu agaji na abinci ba.