Dubban mutane sun yi zanga-zanga a birnin Tel Aviv na Isra’ila inda suka yi kira ga gudanad da bincike kan yaƙin Lebanon. | Labarai | DW | 10.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban mutane sun yi zanga-zanga a birnin Tel Aviv na Isra’ila inda suka yi kira ga gudanad da bincike kan yaƙin Lebanon.

A birnin Tel Aviv na ƙasar Isra’ila, dubban mutane sun yi zanga-zangar nuna ɓacin ransu ga yaƙin da kasar ta yi da ƙungiyar Hizbullahi a Lebanon. Masu shirya zanga-zangar sun ce fiye da mutane dubu 20 ne suka yi jerin gwano a birnin na Tel Aviv, inda suka zargi gwamnatin Isra’ilan da gazawa da kuma gudanad da ayyukan assha a yaƙin da ta gwabza da ƙungiyar Hizbullahi. Sun kuma yi kira ga Firamiyan ƙasar Ehud Olmert, da ministan tsaro Amir Peretz da babban hafsan hafsoshin sojin ƙasar Dan Halutz da su yi murabus.

Wani rukunin sojojin wucin gadin ƙasar na sahun gaba, wajen yin kira ga gudanad da cikakken bincike kan yadda aka tafiyad da yaƙin. Suna zargin shugabannin rundunar sojin ƙasar ne da rashin tsara manufofin shiga yaƙin ma tun da farko, da janyo ruɗami wajen ba da oda da kuma ƙarancin abinci da ruwan sha a duk lokacin yaƙin.