1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban mata a Turkiya sun soki gwamnati

Kimanin masu zanga-zanga 3,000 ne suka fita gangamin adawa da kudirin dokar da ta tanadi cewa masu fyade su auri matan da suka yi wa fyade.

Dubban al'umma ne suka gudanar da zanga-zanga ciki kuwa har da mata da kananan yara a kasar Turkiya, inda a birnin Istanbul suka yi wani cincirindo na adawa da kudirin doka da zai hana daure masu aikata wa yara mata fyade idan sun amince su auresu. Abin da ake ganin salwantar da 'yanci ne.

Kimanin masu zanga-zangar 3,000 ne suka fita gangamin, inda su ka rika waka da kide-kide na adawa da tsare-tsaren gwamnatin ta Turkiya, inda su ke neman da a janye wannan kudirin doka da zai tozarta mata ba tare da bata lokaci ba.

Tuni dai sashin kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya ya fito tare da nuna adawa da tsarin.