Dubban jama'a sun yi hijira daga Bangui
September 26, 2017Talla
Mafi yawan mutanen birnin Bocaranga 15,000 da na Niem 8,000 da ke iyaka da kasar Kamaru sun yi gudun hijira ne a cikin dazukan da ba za su iya samun taimako daga masu ayyukan agaji ba a cewar hukumar ta OCHA cikin wata sanarwa da ta fitar. A ranar Asabar ce dai mayakan 3R suka kai hari a birnin na Bocaranga, duk kuwa da kasancewar dakarun Majalisar Dinkin Duniya na MINUSCA a kasar.
Sa dai wata majiyar soja ta sanar da cewa lalle akwai mutanen da suka mutu, amma cikin yanayin da ake ciki yanzu akwai wahala a san adadin su da kuma na wadanda suka jikkata. Kungiyar ta 3R dai ta bullo ne a shekara ta 2015 a yankin Arewa maso yammacin kasar, inda take ikirarin bai wa al'ummar yankin kariya daga hare-haren 'yan Anti-Balaka.