DRC ta cika shekaru 50 | Siyasa | DW | 29.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

DRC ta cika shekaru 50

Duk da cewa Jamhuriyar Ɗemokraɗiyyar Kwango ta cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai, amma har yanzu tana fiskantar matsaloli da maƙobtanta.

default

Joseph Kabila da Paul Kagame

A dai dai lokacin da Jamhuriyar Ɗemokraɗiyyar Kwango ke cika shekaru 50 da samun yancin kai, har izuwa yanzu dangantakarta da maƙobtanta bai dai dai tu ba, hakan kuwa baya rasa nasaba da yadda ƙasashe maƙobta dama turawan yamma suka yi ta ɗibar ganima a ƙasar, wanda Allah a albarkaceta da arzikin ƙarƙashin ƙasa.

Ɗibar ga nima da kuma fashi da makami shine abinda ke kan gaba idan dai aka yi magana kan tarihin Jamuhuriyar Ɗemokraɗiyyar Kwango. Da farko dai turawan ƙasar Portugal ne suka yi amfani da ƙasar amatsayin han'yar da suke safarar bayi, kana gabanin samun yancin kanta, turawan ƙasar Beljiyum suka yi mata mulkin mallaka. Bayan samun 'yancin kai sai kuma ta faɗa hannun mulkin kama karya na marigayi shugaba Mobutu. A yanzu haka ana yaƙi a gabashin ƙasar, wanda kuma 'yan ƙasashen wajene ke amfani da mayaƙan don ɗibar arzikin ma'adinai na maƙobciyar tasu. Farfesa Georges Nzongola wani ɗan ƙasar ta Kwango ne dake koyarwa a jama'ar North Carolina, inda yace idan ya dubi abinda ke faruwa a ƙasarsa, ta yadda maƙobta ke ci da gumin yan Kwango yana damunsa.

"Banban matsalar itace, ƙasar ta Jamuhiriyar Kwango tana da rauni. Don hakane kawai yasa har 'yar mitsitsiyar ƙasa kamar Ruwanda za ta iya shiga har ta mamaye ƙasa Kwango dake da girma kamar wata nahiya, har ta samu ɗibar ganima a cikinta"

Wani rohoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, ya bayyana cewa har a wannan lokacin ƙasar Ruwanda tana ɗibar ganima babu akama hannun yaro a yankin Kivu dake gabacin jamuriyar Kwango, inda ake zargin 'yan tawayen dake gabacin ƙasar suna samun goyon bayan Ruwanda.

To amma Thierry Vircoulon darektan ƙungiyar kula da tashe tashen hankula ta ƙasa da ƙasa, ya bayyana cewa kyawtatuwar dangantaka tsakanin Jamhuriyar Ɗemokraɗiyyar Kwango da Ruwanda da aka fara samu, wani ci gabane.

"Wata ƙila suna tunanin to ai ko ba komai suna ganin ana ta ɗibar ma'adinan su izuwa wasu ƙasashe, waɗanda kuma ke samun ribarsa. Bayan haka ai dukkanin ma'adinan kamfanonin ƙasashen wajene ke mallakarsu. Manyan kamfanonin cikin gida biyu dake haƙar ma'adinai, sun samu ɓaraka da gwamnati tun zamanin Mobutu. Ƙila shi yasa Kwango ta fara wannan tunanin"

Dangantaka marar kyau irin wannan itace ƙasar Yuganda, wanda ake taƙaddama da ita kan albarkatun mai dake a tabkin Albert a kan iyakar ƙasashen biyu. Ga batun yaƙin da yan tawayen Yuganda na LRA ke yi, wanda ya tilastawa dubban  mutane tserwa faɗar, suna shiga jamhuriyar Kwango ba takardu, daga ƙasashen Brundi ko Ruwanda. Angola madai akwai taƙaddamar kan iyaka tsakininsu.

Shi dai shugaba Josep Kabila wanda ya lashe zaɓen ƙasar a shekara ta 2005, har yanzu ba shi da iko da ɗaukacin makekiyar ƙasar tasa. To amma yana taƙoƙarin kyawtata dangantaka da maƙobtansa.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Andrian Kriesch

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal