1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyayin mutuwar wani dan fafutika a Kwango

Salissou Boukari
May 19, 2018

Dubban mutane ne suka hallara a ranar Asabar a Mujami'ar 'yan katolika ta birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango domin yin addu'o'i ga marigayi Rossy Mukendi Tshimanga.

https://p.dw.com/p/2y0rE
Unruhen im Kongo
Hoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Marigayi Mukendi Tshimanga, wani babban mai adawa ne da gwamnatin shugaba Joseph Kabila wanda aka harbe a watan Fabrairun da ya gabata yayin wata zanga-zanga.

Wadanda suka hallara domin addu'o'in sun hada da 'yan fafutika, da masu rajin kare hakin jama'a, da 'yan adawa, gami da 'yan uwa da sauran abokan arziki na marigayin, inda suka hadu a babbar Mujami'a da ke arewacin birnin Kinshasa domin tunawa da kokarin da marigayin ya yi wajen yaki da mulkin danniya na kabila a kasar.

Matashi dan shekaru 35 da haihuwa wanda kuma shi ne ya kirkiro tsarin hadin gwiwa na "Collectif 2016", an bindige shi ne har lahira a ranar 25 ga watan Febrairu lokacin da jami'an tsaron kasar ta Kwango suka yi amfani da karfin da ya fice kima kan masu zanga-zangar nuna dawa da shugaban kasar Joseph Kabila.