Donald Trump zai dawo da gidajen yari na CIA | Labarai | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Donald Trump zai dawo da gidajen yari na CIA

Jaridar New York Times ta Amirka ta ce shugaba Donald Trump na shirin amince wa da wani kudirin doka na sake bude wasu gidajen yari wadanda suka yi kaurin suna.

Kudirin na Donald Trump wanda har yanzu fadar White House ba ta tabbatar da shi ba, zai sake dawo da tsarin azabtarwa na fursuna wanda aka soke irin na nutsa mutum cikin ruwa domin tatsar bayanai. Kana kuma kudirin zai amince da ci gaba da kai fursunoni masu ayyukan tarzoma gidan yarin Guantanamo, wanda tsohon shugaban Amirkan Barack Obama ya rufe a shekara ta 2009.