1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump ya soke ganawa da Kim Jong-Un

Gazali Abdou Tasawa
May 24, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka ya soke ganawa mai cike da tarihi da aka shirya za a yi tsakanin shi da Shugaba Kim jong Un na Koriya ta Arewa a ranar 12 ga watan Yunin gobe a Singapour. 

https://p.dw.com/p/2yHZG
USA Nordkorea - Donald Trump und Kim Jong Un - TV
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Jin-man

Shugaba Trump ya sanar da wannan mataki ne a cikin wata wasika da ya rubuta ya kuma aika wa takwaran nasa na Koriya ta Arewa a daidai lokacin da Shugaba Kim Jong-Un din ya sanar da lalata cibiyar gwajin nukiliyarsa ta Punggye-ri da ke a Arewa maso Gabashin kasar. 

A cikin wasikar tasa Shugaba Trump ya bayyana wa takawaransa na Koriya ta Arewar cewa yana ganin ganawar tasu ba ta dace ba a halin da ake ciki yanzu yana mai bayar da misali da abin da ya kira hushi da zafafan kalaman da Shugaba Kim Jong-Un din ya furta a cikin bayaninsa na baya bayan nan. Ya kuma yi kashedi ga Shugaba Kim Jong Un a game daukar duk wani matakin da bai dace ba. 

Sai dai duk da ya ce ya ce za su ci gaba da matsawa Koriya ta Arewar da lamba,Shugaba Trump bai yanke kauna ba ga takwaran nasa na Koriya ta Arewa inda ya ce a duk sanda ya canza ra'ayi to kuwa yana iya tuntubarsa ta hanyar kira ko wasika.