1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dole Turai ta daina yiwa Afirka kallon raini

June 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuJO

A yau ake kammala babban taron majami´ar Evangelika a birnin Kolon tare da wani kasaitaccen bukin addu´o´i. Wadanda suka shirya taron sun ce suna rai sama da mutane dubu 100 zasu halraci bukin addu´o´in na yau. Batutuwan da suka fi daukar hankali a taron na yini biyar sun hada da nuna adalci a huldodi tsakanin kasashen duniya, yaki da talauci sai kuma dangantaka tsakanin Kiristoci da Musulmi. A jiya asabar shugaban Jamus Horst Köhler da shugabar gwamnati Angela Merkel sun halarci gun taron. Dukkan ´yan siyasar biyu sun yi suka game da abin da suka kira girman kai da kasashen Turai ke yiwa Afirka. A jawabin da yayi shugaba Köhler yayi kira ga kasashen Turai da su yi aiki tukuru don yakar halayya irin ta ´yan mulkin mallaka.

“Dole ne mu saurari ´yan Afirka don mu gane bukatunsu da kuma burin da suke son cimma da kansu. Dole mu daina yi musu kallon raini.”

Ita kuma a nata bangare Angela Merkel cewa ta yi bai kamata Turai ta cusawa Afirka ra´ayoyin ta ba.