Dole ne shugabannin EU da na Afurka su saka batun Darfur kan gaba a taron Lisbon. | Labarai | DW | 07.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dole ne shugabannin EU da na Afurka su saka batun Darfur kan gaba a taron Lisbon.

‚Yan majalisun dokokin ƙasashen EU da na Afirka sun yi gargadi ga shugabannin nahiyoyin biyu, cewar zasu juyawa duban farra hulla dake wahala baya, idan har suka ƙi saka batun yankin Darfur cikin muhinman batutuwan da zasu tattauna a zauren taronsu na ƙarshen wannan mako a birnin Libon. ‚Yan majalisu 40 tare da ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam daga ƙasashen EU da Afirka, suka yin wannan kira a cikin wata wasiƙar da suka aikawa shugabannin, da cewar rashin ɗaukan matakan gaggawa kann rikicin yankin, zai kasance tamkar juyawa yankin Darfur baya, inda aka ƙyasce cewar rikici ya yi sanadiyar mutuwan mutane fiye da dubu biyu. Tun a watan Juli ne da ya gabata, Kwamitin Tsaro na MDD ya amince da tura jami’an ta su 2,600 zuwa yankin don maye gurbin jami’an tsaron Tarayyar Afirka dake fama da ƙaracin kayan aiki, wanda kuma har yanzu bai cimma nasara ba.