Dole Isra´ila da daina gina matsugunai a yankunan da ta mamaye | Labarai | DW | 22.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dole Isra´ila da daina gina matsugunai a yankunan da ta mamaye

Ga ra´ayin Falasɗinawa shawarwarin zaman lafiya tsakaninsu da Isra´ila ba su da wata ma´ana idan Isra´ila ba ta daina gina matsugunan yahudawa ´yan share wuri zauna a yankunan da ta mamaye ba. A saboda haka shugaban masu tattaunawa na Falasɗinu Ahmed Qoreiya yayi kira ga Isra´ila da ta dakatar da aikin gina gidajen Yahudawa a Gabar Yamma da kogin Jordan da kuma a gabashin Birnin Ƙudus. A cikin makonnin da suka wuce Isra´ila ta dakatar da aikin gina sabbin gidaje kimanin dubu 10 a arewacin Birnin Ƙudus bayan ta sha matsin lamba daga ƙasashen duniya. To amma ta ci-gaba da aikin gina wasu gidaje 300 a yankin kudancin Birnin Ƙudus.