1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokokin shiga Britania

Mohammed Jameel YUshauDecember 17, 2007

Jami'oi zasu yi asarar kudade sakamakon Dokar shiga kasa

https://p.dw.com/p/Ccuw
Tsarin dokar shiga kasaHoto: Steffen Leidel

Sauye sauyen da gwamnatin Birtaniya zata fito dasu a harkar shige da fice zata sanya dalibai da dama na kasashen waje wadanda suke zuwa karatu Birtaniya kowacce shekara su janye, kamar yadda shugabannin jami’o’in Birtaniyan suka koka .

Idan har aka fara amfani da wadannan dokoki, to kam tabbas jami’o’in na Birtaniya zasu rasa miliyoyin kudade da dalibai suke shigowa da su.

Shugaban kungiyar jami’o’in Birtaniya, farfesa Rick Trainor ya bayyana cewa idan aka fara amfani da wadannan tsauraren matakai na shige da fice, to hakan zai tsanantawa dalibai masu shigowa daga kasashen wajen, kuma tasirin hakan zai kare ne akan martabar ilmi a mataki mafi girma a Birtaniya.

Shugaban kungiyar jami’o’in ya cigaba da bayyana cewa ba karamar asara za a tafka ba domin daliban kasashen waje na taimakawa tattalin arzikin Birtaniya da kudade kimanin fam biliyan biyar.

Shi dai sabon tsarin da gwamnatin take shirin fito da shi, kuma ake son ya fara aiki daga shekara mai zuwa, zai saka jami’o’I su zabi daliban da suke bukata akan kari, sannan kuma su yi musu rijista da ofishin harkokin cikin gida, amma shugabannin jam’o’in suna kokarin su gamsar da gwamnati kan bukatar canza wadannan sauye sauye.

Ko da yake dai akwai wasu bangarori na sauye sauyen da jami’o’in suka amince da su, amma shugaban kungiyar jam’o’in ya bayyana cewa akwai barazana a cikin wadannan sauye sauye da zasu karya ka’idojin cinikayya da tattalin arziki wadanda suka bukaci a yawaita daliban kasashen waje a Birtaniya.

Shugaban hukumar nazari akan gudun hijira Danny Sriskandarajah ya bayyana cewa tabbas kam akwai barazana a sabon tsarin, kuma bai kamata a ce anyi wasa da wannan fanni da ke kawowa Birtaniya kudi ba. Mr Danny ya kara da cewa wannan sabon tsari ba wai kawai jami’o’I zai yiwa illa ba, har ma da bankuna, da kulab kulab na kwallon kafa da kamfanoni wadanda zasu so su dauki kwararru domin yi musu aiki.

Kakakin ofishin harkokin cikin gida ya bayyana cewa mafi yawa daga daliban kasashen waje suna taimakawa tattalin arzikin birtaniya, amma wajibi ne gwamnati ta tabbatar ba a sami sauyi akan hakan ba, sannan kuma ya zama duk wani tsari na gudun hijira zai taimakawa manufofin Birtaniyan ne kawai.

Shi ma kakakin ofishin sabuwar ma’aikatar fasaha da kirkire kirkire ya bayyana cewa za a fito da wannan tsari ne domin daukar dalibai mafiya hazaka.