1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

021008 Frankreich Geheimdienstdatenbank Euranet

Forster, SiegfriedOctober 7, 2008

Wannan dokar tana shan kakkausan suka daga daukacin ´yan ƙasar ta Faransa.

https://p.dw.com/p/FVoG
Shugaban Faransa Nicolas SarkozyHoto: AP

A halin yanzu an shiga wani yanayi a fagen siyasar ƙasar Faransa da ake kwatanta shi da girgizar ƙasa ta siyasa, sakamakon wata doka da gwamnati ta kafa wadda ta tanadi tara dukkan bayanai game da ´yan ƙasar domin amfanin hukumomin leƙen asiri. Dokar da ake yiwa laƙabi da EDVIGE ta na shan kakkausan suka daga ilahirin ´yan ƙasar ta Faransa, domin a garesu dokar ba komai ba ce illa yin katsalanda musamman a cikin rayuwarsu ta yau da kullum da kuma ´yancinsu ta walwala. A cikin shirin na yau za mu duba wannan sabon tsarin tara bayanai ta na´urar komputa wanda talakawan Faransa ke cewa wani kumbon leƙen asiri cikin rayuwarsu ne.

A tarayyar Jamus alal misali babu haram sai abin da aka haramta sannan a Faransa babu halan sai abin da aka halatta. Karin magana irin wannan sun daɗe suna taka rawa a yanayin rayuwa ta walwala da ´yanci tsakanin Faransawa. To sai dai yanzu yanayin siyasa da tsarin zamantakewa a ƙasar ya canza, domin a ƙarƙashin sabon tsarin na tara bayanai da ake kira EDVIGE, kowane ɗan ƙasar ta Faransa na zaman mai aikata laifi ne a idanun ´yan sanda, ko da kuwa ba a taɓa samunshi da aikata wani laifi ko yanke masa wani hukunci bisa karya dokar ƙasa ba. Da farko sabuwar dokar wadda gwamnatin Faransa ta kafa a ranar ɗaya ga watan Yuli, ta tanadi tara bayanai da suka haɗa da launin fata da yawan kuɗin albashi da kuma tarihin kowane ɗan ƙasar dangane da rashin lafiyarsa ko cututtukan da yake fama da su. Jean-Francois Chereque na ƙungiyar ƙwadago ta CFDT wannan ba komai ba ne illa wani abin kunya.

1. „Wannan abu ko kaɗan bai da ce ba. Ban ma ga amfanin da za a samu daga wannan sabon tsarin na tara bayanai ba, wanda ya ƙunshi dukkan bayanai na ɗan ƙasa wanda ya ƙunshi ƙungiyar ƙwadago da ya ke cikinta, tarihi dangane da rashin lafiyarsa ko cututtukan da yake fama da su. Ban ga wata fa´ida a cikinsa ba in banda koƙarin hukuma na amfani da haramtattun hanyoyin don sa ido cikin harkokin talakawan ƙasa ba.“

Ga ɗaukacin masu sukar lamirinta dai gwamnatin Faransa ta wuce gona da iri sakamakon kafa wannan doka suna masu cewa ta saɓa da kyakkyawan yanayin demoƙuraɗiyya da bisa al´ada aka san ƙasar da ita. Masu fafatukar kare ´yancin ´yan Adam da ƙungiyoyin ƙwadago da na ɗalibai na zargin cewa yanzu suna iya shiga cikin tarkon ´yan sanda ba tare da sun sani ba. Haka ka iya sa a ɗauke a matsayin baraza ga tsaron lafiyar ƙasa. Suka ce abin da zai biyo baya shi ne yiwa jama´a katsalanda a harkokinsu na yau da kullum tare da janye duk wani ´yancin walwala na ɗaiɗaikun mutane.

Dokar ta EDVIGE wadda a lokacin hutun bazara cikin sirri aka ba da sanawar kafata yanzu bayan hutun ta zama tamkar wani bam na siyasa. A cikin makonni ƙalilan yanzu mutane sama da dubu 140 suka sanya hannu kan wani kundi na masu adawa da dokar. Wannan matakin ya fara yin tasiri domin gwamnatin Faransa kusan a ce ta yi amai ta lashe kamar yadda aka jiyo ministar harkokin cikin gida Michele Alliot-Marie na yin bayani.

2. „A gaskiya da farko ban ɗauki martanin da jama´a za su mayar game da sabon tsarin tara bayanan na hukumomin leƙen asiri don tabbatar da tsaro a cikin gida da muhimmanci ba. A nawa ra´ayin wannan abu ne da ya dace kuma ban ga dalilin da zai sa a ta da jijiyar wuya game da wannan tsarin ba. To sai dai duk da haka akwai wasu abubuwan dake sanya fargaba a zukatan mutane. Saboda haka zan janye su. Domin yin haka alhaki na ne.“

A dangane da zanga-zangar nuna adawa a dole shugaba Nikolas Sarkozy ya janye wasu batutuwan daga dokar ta EDVIGE. Yanzu ba za a tara bayanai da suka shafi cututtukan mutum ko salon rayuwarsa ba to amma za a ci-gaba da tattara bayanai game da yara ´yan shekaru 13 da haihuwa. To sai dai bayan shekaru biyar hukumomi za su yi nazari ko ya kamata a share bayanan na matasa. Ga shugaban hukumar tara bayanai ta Faransa Axel Türk yanzu an kawo ƙarshen maganar abin kunya na EDVIGE.

3. „Idan ka tara bayanai game da matasa ko yara ´yan shekaru 13 ko 14 ko 15 a cikin kundin tara bayanai na komfuta to ya zama wajibi ka sanya lokacin da za ka iya share waɗannan bayanai kwata-kwata. Dole ne a bawa matasan wata damar sake tafiyar da rayuwarsu. Abu na biyu shi ne da farko abubuwan da suka janyo matsaloli su ne bayanai game da halin rayuwarsu da dai sauransu. Amma yanzu da ya ke an janye waɗannan batutuwan daga cikin bayanan da za a tara, bana ganin da akwai wani dalilin nuna adawa da dokar. Shi ya sa yanzu abin da muka sa gaba shi ne za mu sa ido mu ga an mayar da hankali akan batutuwa mafiya muhimmanci a cikin kundin.“

Amma ga masu adawa da dokar sun ce duk da wannan kwaskwarima da aka yi mata ba ta dace da kundin tsarin mulkin Faransa ba. Mai kula da batutuwan da suka shafi daidaita ´yancin jinsi na jam´iyar ´yan ra´ayin gurguzu Faouzi Lamdawi ya ce a cikin sabon tsarin na EDVIGE har yanzu akwai wasu abubuwa da suka haɗa da ƙabila da jinsi mutum a cikinsa. Ita kuwa jaridar Le Monde wadda ta fi shahara a Faransa, a cikin wani sharhi yabawa ta yi da irin kai ruwa rana da aka yi dangane da tsarin ta na mai cewa a karon farko tun bayan ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, Faransawa sun nuna adawa da shirin tsananta matakan tsaro fiye da kima kana kuma sun kare ´yancinsu na walwala.

Yanzu haka dai kwamitin adawa da tsarin na EDVIGe da ya ƙunshi ƙungiyoyi sama da 800 ya ce zai ci-gaba da adawa da tsarin tara bayanan har sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi. A ranar 16 ga wannan wata aka shirya wani gangami yin ntofin Allah tsine ga tsari sannan a cikin watan Disamba majalisar shawara ta Faransa za ta yanke hukunci bisa dacewa ko akasin haka ga kundin tsarin mulkin ƙasar.