Dokar ta baci don tabbatar da tsaro a Niger | Labarai | DW | 04.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar ta baci don tabbatar da tsaro a Niger

Hukumomin Niger sun kafa dokar ta baci a yankuna bakwai na kasar domin shawo kan hare haren ta'addanci a yankin kan iyakar kasar da Mali.

Gwamnatin Niger ta sanar da kafa dokar ta baci a wasu yankuna na yammacin kasar da ke kusa da Mali bayan mummunan harin da wasu masu fafutukar jihadi suka kai Ouallam da ya hallaka sojoji 16 da raunata wasu 18.

Wata sanarwa da gwamnatin ta bayar a jiya ta ce za'a kafa dokar ta bacin a yankuna bakwai a gundumar Tillaberi da Tahoua.

Sanarwar ta ce yawaitar hare hare a yankunan sun haifar da fargabar tsaro da rashin kwanciyar hankalin al'umma.

Yankunan sun hada da Ouallam da Ayrou da Bankilare da Banibangou da Tillaberi da Tassara da kuma Tilia a jihar tahou.

A yanzu za'a baiwa jami'an tsaro karfin karfin iko da suka hada da binciken gida gida a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A shekarar 2015 ma sai da Niger din ta kafa dokar ta baci a jihar Diffa da ke kudu maso gabashin kasar domin shawo kan munanan hare haren Boko Haram.