Dokar ta ɓace a Bangladesh | Labarai | DW | 24.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar ta ɓace a Bangladesh

Gwamnatin ƙasar Bangladesh, ta sassauta dokar ta ɓacen da ta kafa, a sakamakon tashe-tashen hankula da su ka wakana a ƙasar.

Kakakin jami´an yan sanda, ya ce a wasu birane 6, an ma ɗage dokar kwata –kwata a dalili da kwanciyar hankali da a ka fara samu.

Ranar larabar da ta wuce ne gwamnati Dacca, tare da haɗin kann rundunar soja ta ƙasa su ka kafa dokar ta ɓacen, da zumar kawo ƙarshe borin da ɗallibai su ka tada, wanda ya hadasa mutuwar mutun ɗaya, a cikin arangama da jami´an tsaro.

Wannan shine tashin hankali mafi muni, da gwamnatin Bangladesh ta fuskanta, tun hawan ta kann karagar mulki, a watan Janairu na wannan shekara.