1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar shigar da ´ya´yan jam´iyar Baath cikin ayyuka gwamnatin Iraqi

January 13, 2008
https://p.dw.com/p/Couv

´Yan majalisar dokokin Iraqi sun amince da wata doka ta sake daukar da magoya bayan tsohuwar jam´iyar nan ta Baath a cikin ma´aikatun gwamnati. Shugaban Amirka George W Bush ya yi maraba da wannan doka a matsayin wani gagarumin mataki na sasanta al´ummomin kasar. An kaɗa ƙuri´ar amincewa da wannan doka mai rukunai 30 a majalisar ta hanyar daga hannu. Dokar wadda a hukumance ake kiran ta dokar bayanin aiki da nuna adalci ta tanadi dage takunkumai akan tsofaffin ´ya´yan jam´iyar ta marigayi Saddam Hussein na riƙe muƙaman gwamnati.