1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar kwadago: Faransa ta yi amai ta lashe

Yusuf BalaMay 26, 2016

'Yan kwadagon dai sun shiga kassara aikin samar da albarkatun man fetir da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa da sauran harkokin gwamnati a yayin zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/1Iumm
Frankreich Arbeitsmarktreform Streik der Gewerkschaft CGT
'Yan kwadago na daukar matakai na kassara ayyukan gwamnatiHoto: Reuters/S. Mahe

Firaministan kasar Faransa Manuel Valls ya bude kofa a ranar Alhamis din nan ta yiwuwar samar da sassauci a kudirin dokar kwadago bayan da shirin sauyi a kan dokar ya yi sanadi na shiga yajin aiki da ma zanga-zanga a kasar da ta munana, sai dai ya ce gwamnati ba za ta watsar da shirin da ta ke kan sauye-sauyen ba baki daya.

Mista Valls ya bayyana ta kafar talabijin ta BFM a kasar in da ya ce janye sauyin a tsarin kwadago na kasar ba abu ne da zai yiwuwu ba sai dai gwamnati za ta iya yin kwaskwarima inda ya ke cewar "Mene ne zabi ko kuma wadane zabuka muke da su , janye kudirin dokar? Wannan abu ne da ba zai yiwu ba, ba dai wannan gwamnati ba sai dai wata gwamnati."

'Yan kwadagon dai sun shiga kassara aikin samar da albarkatun man fetir da harkokin zirga-zirgar jiragen kasa da ma tunkarar tashar makamashin nukiliya a zanga-zangar ta kwana guda a ranar Alhamis din nan a fadin kasar.