1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hukunta auren dole a Jamus

Halimatu AbbasOctober 27, 2010

Gwamnatin Jamus ta ƙuduri niyyar sa ƙafar wando guda da masu yi wa 'ya'yansu auren dole.

https://p.dw.com/p/PqF8
Ma'aurata musulmi 'yan kaka gida a Jamus.Hoto: dapd

Majalisar minisocin Jamus tana shirin zayyana wata doka da nufin tsaurara hukuncin da ake yanke wa masu yi wa 'ya'yansu auren dole. A yau Laraba ne gwamnatin Jamus ta fid da wasu kaidoji na hukunta 'yan kaka gida da suka ƙi sajewa da al'uma, kwana biyu kacal bayan da shugabar gwamnati, Angela Merkel ta ayyanar da manufar cuɗanya al'adun Jamus da wasu al'adu daban tamkar abin da ya ci tura. Sabuwar dokar wadda sai ta samu amincewar majalisar dokoki kafin a fara aiki da ita ta tanadi yanke hukuncin ɗauri na shekaru biyar a gidan yari ga duk wanda zai yi wa ɗansa ko 'yarsa auren dole. Sauran sharuɗan da dokar ta ƙunsa sun buƙaci 'yan kaka gida da su ba da shedar da ke nuni da cewa sun halarcin azuzuwan da aka kafa da nufin sajesu da al'uma in ba haka a soke takardunsu na zama Jamus.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu