1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana yi wa mata kaciya a Gambiya

Salissou BoukariDecember 29, 2015

Majalisar dokokin Gambiya ta kada kuri'ar amincewa da wata doka da ke haramta yi wa mata kaciya a wani mataki na kare hakkinsu daga wannan mumunar al'ada.

https://p.dw.com/p/1HVqI
Hoto: picture alliance/Robert Harding

Wannan sabuwar dokar da aka aminta da ita a Yammacin ranar Litinin, ta tanadi hukunci har na shekaru uku a gidan kaso, da kuma tara ta kwatankwacin dallar Amirka 1.300. A cewar Asusun Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yara kanana UNICEF, kasar Gambiya na daya daga cikin kasashe 10 kuma dukanninsu na Afirka inda aka fi yi wa mata kaciya, wanda hakan ya shafi uku daga cikin hudu na matan kasar.

Ana ganin dai wannan sabuwar doka za ta taimaka wajen samar wa matan kasar 'yancin tare da karesu daga wannan muguwar dabi'a da ke da babbar illa ga lafiyarsu a cewar mataimakiyar shugaban kasar ta Gambiya Isatou Njie Saidy yayin da take magana a gaban 'yan majalisun dokokin kasar da suka kada kuri'ar da babban rinjaye.