Dokar hana shan tana sigari a bainar jama´a fara aiki a Jamus | Labarai | DW | 01.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar hana shan tana sigari a bainar jama´a fara aiki a Jamus

A yau daya ga watan satumba dokar da ta haramta shan tabar sigari cikin motocin safa safa na gwamnati da cikin gine gine hukuma ta fara aiki a nan Jamus. Dokar ta kare lafiyar wadanda ba sa shan taba, amma suke shakar hayakinta daga masu sha, ta kuma hana sayarwa matasa ´yan kasa da shekaru 18 taba tare da shan tabar a bainar jama´a.