Dokar hana shan taba ta fara aiki a Faransa | Labarai | DW | 01.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar hana shan taba ta fara aiki a Faransa

A kasar Faransa dokar hana shan taba sigari a bainar jamaa ta fara aiki a wasu sassa na kasar.

Yanzu haka dai an hana shan tabar a dukkanin asibitoci da makarantu,da wuraren aiki.

Hakazalia dokar ta shafi wuraren wasanni da kuma dukkan ababen hawa na haya.

Duk kuma wanda aka kama yana shan tabar a wadannan wurare zai biya diyyar euro 135.

A farkon shekara mai zuwa ne kuma zaa kaddamar da kashe na byiu na wannan doka,a wasu sassa da suka hada da wuraren shan shayi da wurin cin abince da wuraren disco.