Dokar gyara ga harkar lafiya a Amirka | Siyasa | DW | 22.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dokar gyara ga harkar lafiya a Amirka

Yan Majalisar wakilan Amirka sun amince da dokar gyara ga harkar lafiya.

default

Shugaban Amirka Barack Obama tare da mataimakinsa Joseph Biden yayin jawabi kan dokar lafiya.

Bayan tsawon lokaci ana tafka zazzafar muhawara kan daftarin gyaran dokar tsarin lafiya na Amirka wanda shugaba Barack Obama ya gabatarwa Majalisar dokoki da nufin samar da kiwon lafiya ga Amirkawa miliyan 32 waɗanda basu da inshorar lafiya, a yanzu dai ana iya cewa batun ya zama tarihi inda dokar ta sami sahalewar yan majalisar dokoki 219 a ƙuriar da suka kaɗa .

Dokar dai ta sami kaiwa da ƙyar da ƙuriú 219 na wakilan majalisar dokokin yayin da masu adawa da dokar suka sami ƙuriú 212.  An dai tafka zazzafar muhawara tare kuma da adawar da dokar daga yan Jamíyar Republican waɗanda suka ce ba zasu bada kai bori ya hau ba. Ga ma dai abinda shugaban marasa rinjaye na jamíyar Republican a majalisar wakilan John Boehner yake cewa a zauren majalisar jim kaɗan kafin kaɗa ƙuriár.

" Ina rokon kowanne daga cikin ku daga dukkanin ɓangarorin biyu ku biyoni mu haɗa hannu domin kaɗa ƙuriár rashin amincewa da wannan daftarin doka, domin ta haka ne zamu samu sami shawo kan ƙalubalen tsarin harkar lafiya ta yadda zaá kawo martaba da nagarta ga wannan hukuma musamman ma kuma yadda zai dace da burin alúmar Amirka".

Yan Republican ɗin dai sun gaza shawo kan yan majalisun dokoki 37 na demokrats waɗanda suma suka nuna rashin amannan da daftarin kundin tsarin lafiyar, wanda idan da sun yi nasara to kuwa shi kenan daftarin ya mutu murus, sai dai yan Republican ɗin dai sun sami jawo raáyin wasu yan majalisar dokoki 34 na demokrats waɗanda suka goya musu baya. A ƙarshe dai dokar ta tsallake kamar yadda shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi ta yi bayani

" An zartar da daftarin ya sami amincewa. Daga nan ne kuma yan majalisa masu goyon bayan dokar suka kwashe da tafi suna murna".

Demokratisches Tryptichon

Shugabar Majalisar Wakilan Amirka Nancy Pelosi

Babu dai ko da mutum ɗaya na Jamíyar Republican da ya kaɗa ƙuriársa ga daftarin, suna masu kashedin cewa wannan zai haifarwa da Obama sakamako mara daɗi a siyasance bisa laákari da ɗumbin miliyoyin dalolin da zaá kashe akan harkar a tsawon shekaru goma masu zuwa. Sai dai kuma shugaban wanda ake sa ran zai sanya hannu akan daftarin domin zama doka nan da yan kwanaki kaɗan yabawa yan majalisar yayi bisa jajircewar da suka nuna duk da farfagandar da aka riƙa yaɗawa cewa daftarin ba zai je ko ina ba saboda matsaloli da kuma rarrabuwar kawuna a tsakanin yan siyasar.

" Nasarar ƙuriár da aka kaɗa, ba nasara ce ta wata jamíya guda ba, nasara ce ga ɗaukacin Amirkawa kuma nasara ce na sanin ya kamata".

Obama wanda ya shafe tsawon makon da ya gabata yana ganawa da yan majalisun dokokin  ɗaya bayan ɗaya domin samun goyon bayansu ya shaidawa Amirkawa cewa wannan alama ce kuma yar manuniya ga sauyin dake tafe.

Ana dai iya kwatanta daftarin da makamanciyar da tsohon shugaban Amirka Teddy Roosevelt yayi a wancan lokaci wanda ya buƙaci bada kulawa ta lafiya ga tsofaffi da marasa galihu.

Abu muhimmanci ga wannan daftarin dokar dai shine cewa a yanzu mutane miliyan 32 waɗanda basu da Inshorar lafiya da kuma masu ƙaramin ƙarfi zasu tallafin gwamnati domin kula da lafiyarsu.  

Mawallafa :Silke Hasselmann/ Abdullahi Tanko Bala Edita Ahmed Tijani Lawan