Dokar Bush ta shige da ficen baki a taci tura | Labarai | DW | 29.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar Bush ta shige da ficen baki a taci tura

Yan Majalisar dattijan Amurka sun ki amincewa da kudirin dokar shige da ficen baki da shugaba Bush ya gabatar. Matakin kin amincewar da yan majalisar suka dauka na nufin cewa ba zaá yi wani sauyi ga dokokin shige da ficen ba har sai bayan zaben shugaban kasa da zaá gudanar a kasar a shekara mai zuwa. Idan dai da majalisar ta amince da daftarin kudiri, da ya share fagen baiwa yan gudun hijira kimanin miliyan goma sha biyu wadanda ke zaune a Amurka damar asamun izinin zama a hukumace. Shugaba Bush ya gaza shawo kan hatta yan majalisar sa ta Republican wadanda suma suka nuna adawa da kudirin dokar. Yan Republican din da dama na ganin cewa amincewa da dokar ka iya zama tamkar tukwici ne ga mutanen da suka karya doka suke kuma zaune a kasar ba bisa kaída ba.