Dokar aikin Jarida a Afirka Ta Kudu | Labarai | DW | 19.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar aikin Jarida a Afirka Ta Kudu

'Yan jarida sun yi jerin gwanon nuna adawa da dokar takaita aikin su a kasar Afirka Ta Kudu

default

'Yan Jarida a kasar Afirka Ta Kudu sun gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da wani kudurin dokar da ke gaban majalisar dokokin kasar, wadda suka ce idan har ta tabbata, to kuwa dokar za ta baiwa hukumomin damar tsare 'yan jarida bisa bayyana abubuwan da jami'an gwamnati ke son boyewa. 'Yan Jaridun dai, wadanda yawan su yakai 300 sun rufe bakunan su ne da tsumma, suna ta furta kalaman neman kawo karshen abinda suka kira nuna wariya a asirce.

Hukumomi sun tsare wani dan Jarida ne bayan da ya buga wani labarin daya zargi 'yan sanda da cin hanci tare da bayyana kudurin dokar da cewar, za ta sa Afirka Ta Kudu ta zauna daura da Zimbabwe wajen yin rufa rufa game da harkar shugabanci. A yanzu dai hukumomin sun janye tuhumar da suke yiwa dan Jaridar nan mai suna Mzilikazia wa Afrika harma ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters a lokacin zanga zangar. Baya ga kudurin dokar da ke gaban majalisar dokokin, ita ma jam'iyyar ANC da ke mulki a kasar ta Afirka Ta Kudu ta bayar da shawarar samar da wata kotun ladabtar da 'yan jarida.

Sai dai kuma shugaba Jacob Zuma na Afirka Ta Kudu ya ce gwamnatin sa ta kuduri anniyar mutunta 'yancin 'yan jarida a kowane lokaci.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal