Dokar aiki wa matasa a faransa | Labarai | DW | 30.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar aiki wa matasa a faransa

Kotun tsarin mulkin kasar faransa zata gabatar da hukunci na karshe a dangane da dokar kwadago da gwamnatin kasar ta kafa,wanda kuma ya kawo hargitsin makonni a wannan kasa.Dokar dai kamar yadda akayi bayani,nada nufin rage matasa masu zaman kashe wando,ta hanyar samar da damar dauka da korar wadanda aka dauka aiki,idan sunyi wani laifi cikin sauki,wanda ya shafi wadanda shekarunsu basu shige 26 ba.A halin da ake ciki a faransan dai ayayinda dalibai ke cigaba da gudanar da bore,kungiyoyin daliban dana kwadago sunyi kira da a sake tafiya yajin aiki na kasa baki daya a mako mai zuwa.Bugu da kari kungiyoyin sun kuma yi kira ga shugaba Jacques Chirac da yayi amfani da ikon da kundun tsarin mulkin kasa ta bashi,wajen gyaran wannan dokaTuni dai yan majalisa suka amince da dokar,amma shugaban kasa shine mai bada amana na karshe.

 • Kwanan wata 30.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu77
 • Kwanan wata 30.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu77