Dokar aiki da matasa a faransa | Labarai | DW | 06.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar aiki da matasa a faransa

Prime minista Dominique de Villepin na kasar faransa ,yayi kira ga dalibai dake zanga zanga dasu koma harkokin karatunsu,inda ya kara dacewa lokaci yayi da zaayi watsi da rigingimun da suka dabaibaye sabuwar dokar aiki data haifar da rigingimu a kasar.A taron manema labaru daya gudanar ayau dai babu alamun cewa shugaban gwamnatin zai amince da bukatun kungiyoyin ,dangane da janye wannan doka.Ya bayyana cewa anyi wannan doka ne da nufin rage batutuwan rashin aikinyi tsakanin matasa a faransa.Makonni da akayi anata ta gangamin adawa da wannan doka dai ya jefa gwamnatin De Villepin cikin halin haulahi.Zanga zangan kasa baki daya gudana sau biyu a kasar dai ya samu halartan sama da mutane million 1.Matasan dai sunyi dafifi akan titunan kasar inda harkoki na karatu suka tsaya cik ,a kanana da manyan makarantu.
 • Kwanan wata 06.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu73
 • Kwanan wata 06.04.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu73