1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Djukanovic ya lashe zaben Montenegro

Yusuf Bala Nayaya
April 16, 2018

Milo Djukanovic a hukumance a wannan Litinin an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Montenegro inda ya samu kashi 53.9 cikin dari na kuri'un da aka kada baki daya.

https://p.dw.com/p/2w9ey
Montenegro Präsidentenwahlen 2018 | Milo Djukanovic
Hoto: picture-alliance/AA/A. Omeragic

Daga cikin 'yan takara shida na gaba da ke zama baban dan adawa ga Djukanovic wato Mladen Bojanic shi ne ya kasance na biyu da sakamako kashi 33.4 cikin dari kamar yadda sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana a wannan Litinin a Podgorica babban birnin Montenegro.

Wannan nasara dai za ta ba wa Djukanovic dan shekaru 56 daga jam'iyyar 'yan gurguzu ta DPS mai mulki damar komawa bakin aiki bayan ritaya daga ofishin da ya mulka daga 1998 zuwa 2002.