Dinke baraka tsakanin Turkiyya da Amirka | Labarai | DW | 30.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dinke baraka tsakanin Turkiyya da Amirka

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya gana da Shugaba Rcep Erdogan a ziyarar farko da wani babban jami'in gwamnatin Amirka ya kai Turkiyya tun bayan fara mulkin Donald Trump.

Babban burin ziyarar sakataren harkokin wajen na Amirka dai shi ne, a kan gyara ga barakar da aka samu tsakanin Turkiyya da manyan kasashe membobin kungiyar tsaron NATO. Tillerson ya yi ganawar kusan sa'o'i biyu da Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya, kana daga bisani ya sadu da Firimiyan kasar ta Turkiyya Binali Yildirim. Batun kasar Siriya na cikin jadawalin ganawar, inda Turkiyya ke neman sai Amirka ta daina goyon bayan da take bai wa Kurdawan Siriya. A ranar Laraba dai Turkiya ta sanar da kawo karshen ayyukan sojojinta a kasar Siriya, to amma ba ta ce ko za ta janye sojojinta da ke cikin kasar ta Siriya ba.