1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dilma Rousseff ta lashe zaɓe a Brazil

November 1, 2010

Sabuwar shugabar ƙasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana aniyar aiki tuƙuru don ci-gaban ƙasa

https://p.dw.com/p/PvM0
Dilma RousseffHoto: AP

Tarihin gasar cin kofin ƙwallo ta duniya Dilma Roussef ta zama mace shugabar ƙasar Brazil ta farko bayan ta lashe zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu da aka shirya jiya Lahadi a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Rousseff mai shekaru 62 a duniya ba ta taɓa shiga takarar zaɓe a baya ba, sai dai ta kasance majidaɗin shugaban ƙasa mai barin gado, Luiz Inacio Lula da Silva wanda ya samu farin jini a ƙasar ta Brazil. Ta lashe zaɓen da kashi 56 cikin 100 na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, a yayin da abokin hamayarta Jose Sera ya samu kashi 44 cikin 100.

Sabuwar shugabar ƙasar ta yi alƙawarin koyi da shugaba Lula da Silva ta fannin yaƙi da talauci da haɓaka tattalin arzikin ƙasa.

"Zan yi aiki bil haƙƙi da gaskiya ba tare da nuna wariya ba ga dukkanin al'umar ƙasar ba. A yanzu na zama shugabar duk al'umar Brazil gaba ɗaya."

Za a rantsar da Dilma Rousseff a ranar ɗaya ga watan Janeru na shekara ta 2011.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal