1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dilma Roussef za ta je New York

Abdourahamane HassaneApril 20, 2016

Shugabar Kasar Brazil Dilma Roussef wacce ke shirin fuskantsar tsigewa da gwamnatin na shirin kai ziyara a birnin New York a gobe Alhamis domin halarta taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi.

https://p.dw.com/p/1IZJK
Haus Nummer 1 Million Minha Casa, Minha Vida
Hoto: Wilson Dias/ABr/CC BY 3.0 BR

Masu aiko da rahotannin sun ce shugabar wacce za ta dawo ran Jumma'a ko Asabar za ta yi amfanin da wannan dama domin shaida wa duniya cewar 'yan majailisun juyin mulki ne suke son yi mata.Dilma ta jam'iyyar 'yan ƙwadago masu ra'ayin makisanci ana zarginta da karya doka a kasafin kudi na shekara ta 2014 a lokacin da aka sake zaɓenta

Bayan ƙuri'ar da majalisar dokokin ta kaɗa ta amincewa da tsigeta inda a nan gaba 'yan majalisun wakilan suma suka amince kuma aka tabbatar da ta aikata laifin,to mataimakinta shi ne zai gajeta har lokacin da za a yi sabbin zaɓuɓɓuka a shekara ta 2018.