Diffa: Akwai bukatar inganta matakan tsaro | Siyasa | DW | 15.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Diffa: Akwai bukatar inganta matakan tsaro

A wani zaman taron da sarakunan gargajiya suka gudanar a birnin Maine Sorowa da ke a jihar Diffa ne aka jaddada bukatar karfafa matakan tsaro cikin al'umma.

Sarakunan yankin na Diffa gami da makwabtansu na Tarayyar Najeriya, sun hallara domin tattauna batutuwa da suka shafi al'adun al'ummomin kasashen biyu. Tare da kuma inganta su ta yadda za su zama wata madogara ga yakin da ake da masu tada kayar baya.

Taron sarakunan gargajiyar na kasa da kasar na zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar tsaron kasashen kewayen Tafkin Chadi ke gudanar da na ta taron a birnin Diffa, kan yakin da take da 'yan ta'adda na Boko Haram, wadda ta soma tun daga ranar Asabar.

Taron da ke zuwa lokacin da shugabannin kasashen da wannan rikici na Boko Haram ya shafa tare da na kasar Faransa suka gudanar da nasu taron a binin Abuja na Tarayyar Najeriya a kokarin da ake na kawo karshen ta'addanci a yankin.