Dialog KRM | Zamantakewa | DW | 01.05.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Dialog KRM

Shekara guda da kafuwar majalisar dake kula batutuwan da suka shafi musulmi a Jamus.

default

Wolfgang Schaeuble da Bekir Alboga a wajen babban taron addinin musulunci a Berlin

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

A tsakiyar watan Afrilun bara bayan sha´awar da jama´a suka nuna, aka kafa majalisar kula da harkokin musulmi a nan Jamus. Wannan majalisa na zaman wata haɗaɗɗiyar ƙungiyar koli wadda ta haɗe ƙungiyoyin musulmi huɗu a Jamus. Daga cikinsu akwai majalisar tsakiya ta musulmi da majalisar Islama da ƙungiyar Turkawa musulmi mai kula da sha´anin addini da kuma haɗaɗɗiyar ƙungiyar cibiyoyin yaɗa al´adun musulmi. An ɗauki lokaci mai tsawo shugabannin siyasa a Jamus na neman musulmi a ƙasar sun samar da ƙungiya guda wadda zata wakilci mafi rinjaye na al´umar musulmin da ke wannan kasa. Wannan dai shi ne aikin wannan majalisar. Shin wasu nasarori ta samu bayan shekara guda da kafuwarta kuma wace alƙibla ta dosa? Muna ɗauke da karin bayani a cikin shirin na yau.

Madalla. ´Yan siyasa a nan Jamus sun daɗe suna nuna halin ko inkula ga batutuwan da suka shafi musulmi ba tare da nadama ba, saboda dalilin cewa ba wata ƙungiya guda ɗaya mai wakiltar musulmin a wannan ƙasa. Saboda sabanin ra´ayoyi tsakanin kungiyoyin musulmi daban daban, gwamnati ta rasa abokiyar tattaunawa a tsakanin musulmin. Don ganin an ɗauke su da muhimmanci, a dole ƙungiyoyin musulmin suka manta da banbance banbancen da ke tsakaninsu suka haɗa kai waje ɗaya. Da haka ne suka kafa haɗaɗɗiyar majalisa mai kula da batutuwan da suka shafi musulmi musamman do sauƙaƙa tuntuɓar juna tsakaninsu da hukumomin wannan kasa, inji Bekir Alboga wakilin kungiyar Turkawa Musulmi mai kula da sha´anin addini, wanda kuma shi ne tsohon kakakin haɗaɗɗiyar majalisar musulmin.

1. Alboga:

“An ɗauki shekaru masu yawa ana kira garemu da mu kafa wata ƙungiya guda ɗaya tilo wadda zata yi magana da yawun dukkan musulmi a nan Jamus. Hukumomin kasar sun nunar da cewa ta haka ne zasu iya tattaunawa da mu musamman a dangane da shigar darussan adinin musulunci a manhajar makarantun firamare mallakin hukuma. Mu kuma a na mu ɓangaren mun amsa wannan kira.”

An bayyana kafa majalisar mai kula da batutuwan musulmin da cewa babbar nasara ce, musamman bisa la´akari da banbance-banbancen dake tsakanin ƙungiyoyin al´umar musulmin, inji Ali Kizilkaya shugaban majalisar Islama kuma kakakin haɗaɗɗiyar majalisar musulmi har nan da watanni shida masu zuwa.

2. Kizilkaya:

“Samun wannan haɗin kai wani muhimman abu ne mai cike da tarihi. Haka kaɗai ma wata babbar nasara ce. A ɗaya ɓangare kuwa, a cikin shekara guda da kafuwarta wannan majalisar ta ba mu damar ƙara sanin juna tare da bayyana matsayinmu don samun fahimta a tsakani. Mun aiwatar da haka a cikin aikace aikace mu da dama musamman wanda ya shafi batun koyar da darasin addini.”

Yanzu haka dai muhimmin abin da majalisar ta Islama ta sa a gaba shi ne koyar da darasin addinin Islama a makarantun gwamnati. A siyasance ba bu tantama akan haka, to sai dai dole ne da farko a kafa kungiyoyin jihohi waɗanda tare da gwamnatocin jihohin zasu tsara yadda manhajar koyar da addini, domin a nan tarayyar Jamus ko wace jiha ce ke da alhakin tsara harkokin ilimin ta. A cikin shekara guda da kafuwarta majalisar ba ta cimma burinta na samar da manhaja bai ɗaya ta koyar da ilimin addinin Islama ba. To amma  ta duƙufa don ganin haƙanta ya cimma ruwa, inji Alboga sannan sai ya kara da cewa.

3. O-Ton Alboga:

“Nan da watanni kadan masu zuwa zamu amince da tsarin mulkinmu don ba da damar kafa rassan majalisar a jihohi. Shi yasa nan ba da jimawa ba jama´a zasu ga matakin farko da za´a dauka.”

Matsayin musulmi a Jamus da tasirinsu a fannoni siyasa da zamantakewa ya samu wani sabon kwarjini sakamakon kafa majalisar kula da harkokin musulmin. Yanzu dai sun daina magana a matsayin ɗaiɗaikun ƙungiyoyi, a´a da murya ɗaya suna ƙoƙarin yiwa jama´ar ƙasar bayani game da manufar majalisar. Muhimman abu a nan shi ne bawa dukkan ƙungiyoyi daraja iri daya ba tare da nuna fifiko kan wasu ba. Burin al´umar musulmin a Jamus shi ne su samu cikakkiyar amincewar ´yan siyasar kasar a matsayin abokannen tattaunawarsu, inji Ali Kizilkaya.

4. Kizilkaya:

“A daraja mu kamar yadda ake yiwa sauran ƙungiyoyin addini. To amma abin baƙin ciki shi ne har yanzu ba a kai wannan matsayi ba. Alal misali in ban da babban taron Islama ba, ban ga in da hukuma ta ƙauki musulmi a matsayin abokin tattaunawarta ba. Wannan abin baƙin ciki ne. Muna son a amince da mu a matsayin ´yan kasa da suka san ciwon kansu kuma suka kasance wani ɓangare na wannan jama´a. Yin haka zai hanzarta shigar da musulmi a cikin harkokin yau da kullum na wannan ƙasa.”

Tun bayan kafuwarta majalisar ta yi ta shan suka kan cewa kashi ɗaya cikin biyar na al´umar musulmin wannan ƙasa ta ke wakilta. Wasu kuma na masu ra´ayin cewa wasu ƙungiyoyi dake cikinta masu adawa ne da tsarin demoƙuraɗiyya. Ali Kizilkaya ya ce wannan zargin ba da tushe bare makama. Ya ce majalisar ta amince da ´yancin walwala irin na tsarin demoƙuraɗiyya, ta na watsi da tarzoma sannan ya jaddada cewa kimanin kashi 85 cikin 100 na gamaiyar masallatai na da wakilci a cikinta wato kenan majalisar na zaman wakiliyar mafi rinjaye na musulmai a Jamus.

5. Kizilkaya:

“Dole ne dukkan musulman da ke da burin tafiyar da addininsu da samun ´yancinsu na kungiyoyin addini su haɗa kansu. Mun hada kanmu kuma mun cike dukkan ƙa´idojin tsarin mulkin wannan ƙasa shi yasa hukuma ba zata iya zaɓan mana wanda zai wakilce mu ba.”

Su kansu wakilan wannan majalisa sun san cewa har yanzu mafi rinjaye na Jamusawa na ɗari-ɗari da addini saboda haka dole sai an tashi tsaye wajen wayar musu da kai don kawad da bambamce bambamcen da ake samu a tsakani. Saboda haka shiga tattaunawa da majami´u da sauran al´ummomin da ba ruwansu da addini ya zama wani ɓangare na aikin wannan majalisar. Shugabanninta sun nunar da cewa zasu ci-gaba da tattaunawa da sauran mabiya addinai daban daban domin hadin kan al´adu da addinai na daya daga cikin shika-shikan samar da zaman lafiya tsakanin al´umma.