Deustche Afrika Energy Konferenz | NRS-Import | DW | 30.04.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Deustche Afrika Energy Konferenz

Hannover Messe 2008: Tawagogin Afirka da na Jamus sun yi mahaurori a game da cinikiyar makamashi albarkacin taron baje kolin Hannover

default

Cinikin iskan gas tsakanin Afirka da JamusRanekun 23 ga 24 ga watan Maris na shekara ta 2008 a ka gudanar da taron ƙoli karo na ukku a game da batun makamashi tsakanin Nahiyar Afirka da Jamus.

Ƙungiyar ´yan kasuwar Jamus masu mu´amila da Afrika wato Afrika Verein, ta shirya wannan haɗuwa albarkacin  bikin Hannover Messe na shekara shekara, wato baje kolin da ya fi girma  a duniya baki ɗaya ta fannin nuna husa´o´in kamfanoni da masamna´antu, da kuma cinikayya.

A yinin farko, taron ya wakana a cibiyar kasuwaci ta birnin Hamburg.

Sai kuma yini na biyu, a tsakiyar harabar taron baje kolin Hannover Messe.

An samu wakilai daga ƙasashe da dama na Afrika, wanda suka haɗa da Tarayya Nigeria, Algeria Tunisiya, Kenya, Kongo, Cote d`Ivoire, Burkina Faso, Guinee da dai sauransu.

A ɓangaren Jamus kuwa, kamfonin dake kula da sarrafa makamashi kamar su E-On, Oil tanking, Lahmer International, EnBW da dai makamantansu, sun halarci taron, wanda ya kasu a rukunai guda biyu.

Rukunin farko yayi mahaurori  a game da makamashin da ya shafi man petur da Gaz, sai kuma na biyu wanda yayi tunani a game da makashin da ake samu ta hanyar sarrafa hasken rana, iska mai kaɗawa,  tsirrai da kuma ruwa.

Daniel Muthmann, shine mataimakin shugaban kamfanin samar da makashi na E-on, wanda yayi suna a nan Jamus da ma Turai baki ɗaya ta fannin cinikiyar iskan Gaz.

Ya na kuma ɗaya daga cikin wanda suka gabatar da jawabai a game da mu´amilar makashi tsakanin Afrika da Turai da kuma wajibcin ƙara ƙarfafa ta, ya na mai cewar:


Idan aka fidda Russia da wasu yankuna na Asiya inda kamfanin mu ke da hulɗodi masu ƙarfi, Afirka ce ta gaba, wajen gudanar da hada-hada tare da mu, wannan Nahiya na taka rawar gani a game da cinikiyar gaz da Turai.


Jami´an ya bitar ɗimbin albarkatun makamashi da Afrika ta ƙunsa to saidai duk da haka, itace ƙutal ta fannin wadatuwar jama´a  a game da hasken wutar lantarki da yin amfani da gaz a cikin gidaje ya bayyana wajibcin ƙara saka jari a nahiyar, ta yadda za a magance wannan matsala:Idan aka duba Afirka, Kamfanoninmu sun gudanar da bincike, sun kuma tabbatar da albarkatu masu yawa na Gaz, wanda aka gano, da ma wanda har yanzu ba a gano ba.

Saboda haka, Afirka yanki ne dake buƙatar saka jari, da kuma tallafawa kamfanonin cikin gida da husa´ar zamani don ƙara ƙarfafa bincike.


Wasu daga mahaurorin da aka tabka a wannan dandalin ,sun haɗa da ayyukan raya ƙasa da kamfanonin ke gudanarwa don kyauttata rayuwar jama´a  a ƙasashen da suke aiki, ta wannan fannin ma kampafanin Eon ya cencenci yabo inji wakilinsa a taron Hambourg.

Kamfaninmu a cikin siyasarsa na yin la´akari da ayyukan gine-ginen asibitoci, makarantu, da sauran abubuwa na more rayuwar jama´a.

Akwai cikkakar shaida a ƙasar Russia, inda muka share shekaru 30,duk da cewar a wannan ƙasa al´umma ba ta cikin irin wannan matsaloli.

Idan muka samu sa´ar ƙulla hulɗoɗi da Afrika, ko shakka babu al´umma za ta ci moriya.

A shekara bara, Equatorial Guinea ta zaɓe mu a matsayin abokan hulɗar Gaz , haka zalika, ƙasar Nigeria, sabuwar mu´amila tsakanin Nigeria da Jamus ta fannin makamashi ta zama kyaukyawan misali na hulɗoɗi tsakanin Turai da Afrika.


Baki ɗaya mahalarata taron makamashi tsakanin Jamus da Afirka sun cimma matsaya guda,  a game da cencentar yanayin da ake ciki, domin haɓɓaka al´ammuran makamashi a nahiyar Afirka.

Sun bada hujjoji dabam dabam, wanda suka haɗa da sabuwar taswirar da ƙungiyar Tarayya Turai,da ƙasashen G8 suka ɗauka wajen yaƙi da ɗumamar yanayi ta fannin samar da wasu sabin kafofi na makamashi, wanda ba su gurɓata yanayin.

Sannan da dama daga gwamnatocin Afirka sun tanadi hanyoyin doka, wanda suke baiwa kamfanonin ƙetare damar gudanar da ayyuka cikin walwala da tsaro.

A ɗaya wajen,  ƙiddidigar masana tattalin arziki ta gano cewar, arzikin Afirka na bunƙasa fiye da ƙima, a saboda haka, Afrika na buƙatar ƙarin makashi domin tafiyar da kamfanoni da masana´antu, ga buƙatocin haskaka birane da ƙayuka, da kuma wadatar da su da iskan Gaz, saboda haka mahalarta taron,sun yi kyaukayawan fatan ganin, an yi amfani da wannan taro don cimma wannan buri.

Abel Tella, shine Sakatare Jannar na Ƙungiyar ƙasashen Afrika masu samar da makashi da jigilar sa da kuma rarraba shi wato Ƙungiyar nan ta UPDEA, ya nuna wajicin haɗin kan Afrika don fuskantar kasuwannin duniya na makashi ya ce,idan Afrika na buƙatar cin moriya kasuwancinta na makamashi da ƙasashen duniya, ya kamata ƙasashen Afrika su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Ɗaukar irin wannan mataki, zai taimakawa Afirka, ta saida makamashinta da daraja, sannan ta warware matsalolin da ta ke fama da su cikin gida ta fannin wutar lantarki.


A ɗaya wajen, Sakatare Jannar na UPDEA, ya bayyana mahimmancin  taron da ya haɗa Jamus da Afirka, a game da batun makashi, ya kuma buƙaci sauran ƙasashen Turai suyi koyi da Jamus ta fannin cuɗɗaya da mu´amila tare da Nahiyar Afirka:

Jamus ta bayyana matuƙar shawar ƙulla mu´amila da Afirka, ta fannin cinikayar makamashi, saboda haka, wannan taro a ganina, zai tabbatar da wannan buri.

Karo na ukku kenan aka shirya irin wannan haɗuwa, kuma ako wace shekara, mahalarta daga ɓangarorin biyu na ƙaruwa.

Saboda haka, ba ni da shakku , a game da alfannon taron, ta fannin cigaban tattalin arzikin Afrika.