Denmark ta umarci ´yan kasar da su fice daga Lebanon | Labarai | DW | 05.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Denmark ta umarci ´yan kasar da su fice daga Lebanon

Gwamnatin Denmark ta yi kira ga ´yan kasar ta da su fice daga Lebanon bayan wani hari da masu zanga-zanga suka kai kan karamin ofishin jakadancinta dake birnin Beirut. Wata sanarwa da ma´aikatar harkokin waje ta bayar ta yi kira ga dukkan ´yan Denmark da su kasance a cikin gidajensu har sai an kammala shirye-shiryen kwashe su daga Lebanon. A yau ´yan zanga-zanga a Beirut suka cunna wuta a gidan da ofishin jakadancin Denmark yake tare da kai hari kan gidajen kiristoci dake kusa don nuna fushinsu dangane da zane-zanen batanci ga Annabi Mohammad SAW da wata jaridar Denmark din ta buga. Rahotanni sun ce akalla mutane 28 sun samu raunuka a zanga-zangar. Yanzu haka malaman addinin islama na kokarin kwantar da hankalin jama´a. A jiya asabar ma masu zanga-zanga a Damaskus babban birnin Syria sun cuna wuta a ofisoshin jakadancin Denmark da Norway. A Afghanistan kuwa an gudanar da zanga-zangar ce cikin lumana.