Denmark ta gargadi ´yan kasar da su fice daga Indonesia | Labarai | DW | 12.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Denmark ta gargadi ´yan kasar da su fice daga Indonesia

Bayan ta janye ofisoshin jakadancinta da sauran jami´an diplomasiyan ta daga kasashen Indonesia, Iran da kuma Syria saboda damuwa ga lafiyarsu, gwamnatin Denmark ta ta yi kira ga ´yan kasarta da su fice daga Indonesia saboda dalilai na tsaro. Ma´aikatar harkokin wajen Denmark ta ce yanzu haka ma´aikatan ofishin jakadancin ta sun fice daga Syria na wani gajeren lokaci bayan an yi musu barazana. A makon da ya gabata masu zanga-zangar nuna fushi da buga zane-zanen tozarta Annabi Mohammed SAW da wata jaridar Denmark ta fara yi, sun kona ofishin jakadancin kasar dake birnin Damaskus. Har wayau dai ana ci-gaba da gudanar da zanga-zangar yin tir da cin mutuncin al´umar musulmin. A jiya asabar dubun dubatan musulmi sun gudanar da jerin zanga-zanga a biranen London, Paris da kuma Düsseldorf.