Denmark ta cafke musulmi 8 bisa zargin shirin kai mata hari | Labarai | DW | 04.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Denmark ta cafke musulmi 8 bisa zargin shirin kai mata hari

´Yan sandan kasar Denmark sun ce sun bankado wani shirin kaiwa kasar wani harin bam. Hukumar leken asirin kasar ta ce a wani samame da aka kai cikin daren jiya an kame mutane 8 wadanda ake zargi da shirin aikata ta´addanci da kai hare haren bama-bamai. Ana kuma zargin mutanen da alaka da kungiyoyin ´yan ta´adda na kasa da kasa ciki har da Al-Qaida. Shugaban hukumar leken asiri ya fadawa manema labarai a Copenhagen babban birnin kasar ta Denmark cewa dukkan wadanda aka kaman matasa ne ´yan shekaru tsakanin 19 zuwa 21. Ya ce an shafe lokaci mai tsawo ana sa ido akan mutanen. Wannan dai shi ne karo na 3 cikin shekaru biyu da ´yan sandan Denmark suka cafke mutane akan zargin shirin aikata ta´addanci.