Davos Börse | NRS-Import | DW | 23.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Davos Börse

default

Taron Davos

  A yau ne wakilai daga ƙasashe dabam- dabam na dunia, wanda su ka haɗa da  da shugabanin  kamfanoni fiye da 100 na dunia, suka fara taron shekara sheka a Davos na kasar Suiz. Mahalarta wanan taro sun fara da wata zazzafar mahaura a game da faɗuwar hanayen jari  a hada-hadar kasuwannin dunia, wakilin DW Marco Vollmar ya halarci zauran taron, ya kuma aiko rahoto, wanda Yahouza Sadissou Madobi ya fassara mana.◄
Kamar yadda  su ka saba  ako wace shekara, a bana ma masana harakokin tattalin arziki da shugabanin kamfanoni da na gwamnatoci daga sassa dabam-dabam na dunia, sun kiri taro a Davos dake ƙasar Suiz. Saɓanin shekarun da su ka gabata, mahalarta taron na Davos sun fara da wata mahaurori, a game da faɗuwar hanayen jari a kasuwwanin dunia. Ƙurrarun masana ta fannin harakokin tattalin arziki, sun bayyana ra´ayoyi iri ɗaya a kan cewar babu maganin dindindin ga abkuwar taɓarɓarewar hanayen jari a hada-hadar yau da kullum cikin kasuwwanin dunia, to saidai duk da haka akwai hanayoyin  riga kafi kamar yadda Klaus Kleinfeld, tsofan shugaban kamfanin Siemens, wanda a halin yanzu, ke riƙe da matsayin shugaban hukumar ƙoli ta kampanin Alcoa na ƙasar Amirka ya bayyana. " A gani na magani  warkas da matsalar faduwar hanayenjari har kullum iri guda ne,wato kamfanoni sun himmantu wajen ƙirƙire da kuma ingata kaya tare da sayar da su cikin parashe mai rahusa. Wannan shine ɗaya daga tubalin da tattalin arzikin ƙasar Jamus yayi dogaro a kansa". Shima Jürgen Großman saban shugaban kampanin wuta da ruwa na Jamus wato RWE ya bayyana irin wananra´ayi tare da cewar: "Ta kamata mu kara duba hanyoyin kyauttata parashe da kuma na saka hanayen jari. A lokata da dama a ka fuskanci kura-kurai masu yawa ta wannan fannonin. sannan a cikin wannan yanayi da tattalin arzikin dunia ya shiga matsayi ƙaƙa ni kayi, ba ta kamata ba mu yi fargaba ba, ya zama wajibi mu nutsu, mu sami hanyoyin kuɓuta daga wannan mastala". Gobara da ta faro daga Amurika a cikin harakokin hanayen jari,ba da wata-wata ba,  ta ɓulla a sauran ƙasashen dunia, ta la´kari da mu´amilar cinikaya mai ƙarfin gaske, da ta haɗa ƙasar da sauran sassa na dunia. To saidai a cewar Wang Zhou Jian shugaban kamfanin sadarwa na China Mobile, wannan matsala ba ta yi ƙarfi ba a ƙasashe kamar China da India. " wannan al´amari ya zuwa yanzu, bai shafi China ba, wadda har yau ke ci gaba da samun angizo mai ƙarfi ga tattalin arzikin ƙasashen dunia." Mahalarta taron Davos sun buƙaci wanda ke da hannu a cikin harakokin hanayen jari da ƙayyade farashe a dunia, su daina ƙarin gishiri ga abunda ya faru ga tattalin arzikin dunia, sannan  su maida himma, domin kawo ƙarshen al´amarin kafin ya zama gagarabadau. David O´Reilly shugaban hukmar zartasawa ta kamfanin  Chevron Corporation na kasar Amirka ya nunar da cewar Amurika za ta iya ƙoƙarinta, domin taka birki ga wannan matsala. "Ina tsammanin cewar tattalin arzikin Amirka da kansa za samo hanyoyin fita daga wannan ƙangi, ƙila ma cikin lokaci ƙalilan. sannan ina daga masu tunanin cewar ilolin da wannan taɓarɓarewa ta jawo a sauran ƙasashen dunia ba ta kai mizanin da ake kaita ba."