1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

David Cameron ya yi murabus daga majalisa

Abdul-raheem HassanSeptember 12, 2016

Tsohon firaministan Burtaniya David Cameron ya sanar da aniyarsa ta yin murabus daga majalisar dokokin kasar ba tare da bata wani lokaci ba.

https://p.dw.com/p/1K0m4
Großbritannien David Cameron Premierminister
Hoto: picture-alliance/dppa/A. Vitvitsky

Tsohon Firaiministan Birtaniya David Cameron ya yanke hukuncin sauka daga mukaminsa na majalisar dokoki a wata sanarwa da ya fidda a wannan Litinin din inda labarin ya zo wa 'yan Burtaniya din da ba zata. A farko dai David Cameron ya fara yin murabus ne a matsayin sa na Firaiminstan Birtaniya a watan Yuni bayan da ya gaza shawo hankalin 'yan kasar da ga kudirin su na yin zaben raba gardama na ficewa daga tarayyar turai, dama dai Cameron ya kudiri aniyar raba kansa da shugabanci a mulkin jam'iyar Consertive da ake ganin Theresa May ke rowa da tsaki a batun raba gari da kungiyar EU.