1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta yanke wa Mladic daurin rai da rai

Ramatu Garba Baba
November 22, 2017

A wannan Laraba, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta zartas da hukuncin daurin rai da rai kan Ratko Mladic tsohon jagoran Sabiyawan Bosniya bisa laifin hannu a kisan kiyashi.

https://p.dw.com/p/2o4BI
Niederlande Urteil Ratko Mladic
Hoto: Getty Images/M. Porro

Kotun ta ce ta sami Mladic da aikata laifukan yaki a kisan kiyashin da sojoji suka yi wa Musulmin Bosniya a garin Srebrenica a 1995. Kotu ta kwashe shekaru fiye da biyar ta na binciken laifin da aka tuhumi jagoran Sabiyawan mai shekaru 75 a duniya bisa laifin cin zarafin bil'adama a lokacin yakin Bosniya da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane dubu dari daya da kuma raba wasu fiye da miliyan biyu da matsugunansu.

Daga cikin wadannan alkaluman akwai Musulmi akalla dubu takwas da aka tabbatar da mutuwarsu a arewacin Srebrenica na yankin Balkans. Ratko Mladic na da damar daukaka kara inji kotun.