1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daurin rai da rai kan sojin Turkiyya 42

Ramatu Garba Baba
October 5, 2017

Wata kotu a Turkiyya ta yankewa wasu tsoffin sojojin kasar 42 hukuncin daurin rai da rai bayan samun su da hannu a kitsa makircin hallaka shugaba Recepp Tayyib Erdogan.

https://p.dw.com/p/2lE7q
Türkei Nach Putschversuch lebenslange Haft für Soldaten
Hoto: Reuters/O. Orsal

Alkali Emirsah Bastog ya ce mutane 42 da akasarinsu sojoji ne na daga cikin mutane 47 da aka gudanar da shari'a a kansu bisa yunkurin hallaka Shugaba Erdogan. Sai dai bai anbato hukuncin da ya rataya a kan Fethullah Gulen ba, shehin malamin nan da ake zargi da shirya juyin mulkin daga Amirka inda ya ke samun mafaka ba.

Shugaba Erdogan da iyalansa sun yi nasarar tsira da ransu daga ginin wani otel bayan da sojoji suka yi wa wannan ginin dirar mikiya a daren da aka yi kokarin kifar da gwamnatinsa. Mutane fiye da 200 ne suka rasa rayukansu a ranar 15 ga watan Yulin bara a gumurzun juyin mulkin.