Daular Oman: Karshen zaman jin dadi da walwala
Dukkan shugabannin Larabawa da suka yi shekaru kan mulki a guguwar 2011 an tayar musu kayar baya. Amma ga sarkin Oman da ya kwashe shekaru kan mulki har yanzu yana da matukar farin jini a tsakanin jama'arsa.
Masarauta a duniyar Larabawa
Bashi da aure bai da 'ya'ya: Qabus bin Said al-Said mutum ne na daban cikin sarakunan Larabawa. Sama da shekaru 40 yake mulkin kasar Oman, wato ya fi ko wane sarki a kasashen Gabas ta Tsakiya dadewa kan mulki. A ranar 18.11.2015 ya cika shekaru 75 da haifuwa kuma ranar ce ya yi bikin cika shekaru 45 kan kujerar mulki.
Bunkasa cikin sauri
Sultan Qabus a karamin lokaci ya maida Oman cikin tsarin zamani. Kafin shekaru 45 da suka gabata Daular Oman na cikin mafiya talauci a kasashen Larabawa. Amma a yanzu Oman tana cikin kasashen duniya da ke da ci-gaban tattallin arziki a bisa kiddigar MDD. Watakila hakan na alaka da fara hakar mai wanda Oman ta soma a shekarun 1960.
Fice a tukin jirgin ruwa
Cikin kayakin tarihin kasar, Oman ta yi suna wajen arzikin tagula. A karni na 17 izuwa 18 Daular Oman ta yi yake-yake, inda ta mamaye wani bangaren kasashen gabar tekun gabashin Afirka, ciki harda mamaye tsibirin Zanzibar. Amma dai a kwana a tashi an kawo karshen wannan mamayar. Inda kuma daga nan kasar ta bace a lissafin siyasa da tattalin arzikin duniya.
Daga tsohon zamani izuwa zamanin yau.
Gabanin shekaru 45 da suka gabata babu hanyar kwalta in banda Muskat babban birnin kasar. Wutan lantarki da ruwan sha a wancan lokaci ba su wadata ba. A yanzu Oman ta shimfida kwalta kusan a ko wane lungu da sakon kasar. Bugu da kari akan samu asibitoci da makarantu har cikin karkara, kuma yanzu haka kasar na da manyan makarantu da jami'o'i sama da 20.
Ci gaban mata
Gwamnatin Oman tana matukar baiwa bangaren mata mahimmanci. Mata na walwala yadda suke so kuma ana ba su damar karin ilimi da yin aiki. Misali a jami'ar gwamnati ta Sultan Qabus, akwai wani tsarin kaso maza da mata, inda matan ke matukar samun sakamako mai kyau a jarrabawa fiye da 'yan uwansu dalibai maza.
Tarin hamada
Kasar mai mutane kimanin miliyan hudu, Oman na cikin kasashen duniya da ke da karancin matsuguni, sabo da kasancewar rabin kasar duk hamada ta mamaye shi. Kasancewar arzikin man kasar da ke shinfide bai da yawa, hakan ya sa gwamnati neman wata hanyar samun kudin shiga kamar harkar yawon bude ido.
Gina kasa da ababen marmari
A cikin shekarun da suka gabata Oman ta kasance kasar da masu yawon shakatawa suka fi sha'awa. A tashar jiragen ruwan Muskat ana samun kwale-kwale da ke tsallakawa da jama'a. Hada ababen gargajiya da kuma gina otel na zamani, suna matukar jawo hankalin masu ziyarar bude ido da shakatawa. A yanzu ana kan gina tashar jiragen ruwan Muskat kuma wasu sabbin otel za su biyo baya.
Matsalolin tattalin arziki
Yawon shakatawan dai ba zai iya maye gurbin karancin mai da ake haka ba. Da jimawa kasar ba ta iya cika burin kudin shiga da take yin kiyasin samawar daga cikin gida ba. Don haka batun tattalin arziki ya zamewa Oman wani babban kalubale. Al'ummar kasar na bunkasa, bukatu kuwa sai karuwa suke yi.
Karuwar matasa
A ko wace shekara dubban matasan Oman ke kwarara wajen neman aiki, mafi yawansu suna dauke da shaidar kammala karatun jami'a. Akasarin matasan na son aikin gwamnati, domin ya fi kamfanoni masu zaman kansu albashi mai tsoka.
Tarzoma a daular
A lokacin guguwar sauyin kashen Larabawa, Oman ita ma ba ta tsira ba. Dubban mutane suka yi boren neman a yaki cin hanci kana a inganta musu rayuwa. Bayan tattaunawa cikin gaggawa da mika wuya kan sauye-sauye, gwamnati ta yi nasarar shawo kan lamarin cikin karamin lokaci. A lokacin arangamar mutun guda ya mutu, abinda ya kada kasar baki daya, domin ita ce ake ganin mai kula da hakkin jama'a.
Addinin Islama
Akasarin musulman Oman basa bin mashabar Sunni ko Shi'a, don su suna bin wata darika ce da ake kira "Ibadiya" Daya daga dalilan da yasa Sarkin kasar ke shigewa gaba a sasanta musulman yankin. Babban misali shi ne shiga da Oman ta yi a sasanta rikicin nukiliyar Iran da kasashen yamma, da kuma rawar da kasar ke takawa wajen sako mutanen da kungiyoyi masu kaifin bin addi ni ke sacewa a yankin.
Ayoyin tamba kan mai gadon mulki,
Ana bikin murnar ciki shekaru 45 kan mulki har yanzu shugaban na da farin jini, inda ake ganin hotunansa a rigunan 'yan kasar. Kuma duk da shekarun da ya yi a mulki, har yanzu yana da cikakken iko a mulkin. Amma a yanzu babu wanda ya san wa zai gaji sarkin da bai taba haifuwa ba. Wannan shi ne kalubalen da ka iya faruwa cikin shekaru da ke tafe.