Dauki ba daɗi da mayakan Taliban a Afghanistan | Labarai | DW | 23.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dauki ba daɗi da mayakan Taliban a Afghanistan

Dakarun sojin Britaniya dake kudancin ƙasar Afghanistan sun yi ɗauki ba daɗi da mayakan Taliban domin taimakawa sojin Afghanistan da jamián yan sanda murkushe farmaki da yan Taliban ɗin ke kaiwa a lardin Helmand. Ɗauki ba daɗin wanda ya shafe tsawon saói takwas ana gwabzawa, a cewar rahotanni, sojojin Afghanistan ɗin goma sha uku tare da yan Taliban tara suka rasa rayukan su. A wannan watan ne dai sojin Britaniya suka karɓi jagorancin ƙungiyar tsaro ta yankin tekun atlantika NATO wadda za ta cigaba da kula da shaánin tsaro a kudancin Afghanistan inda ake sa ran tura dakarun sojin Britaniya 3,000 zuwa yankin. Kudancin ƙasar ta Afghanistan shi ne mafi ƙarancin tsaro tun bayan da yan Taliban suka ƙaddamar da hare hare a yankin .