Dattin masana′antu a Abidjan na daga cikin abin da aka yi sharhi kansu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 15.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Dattin masana'antu a Abidjan na daga cikin abin da aka yi sharhi kansu

Jaridun Jamus sun yi kakkausan suka akan jibge datti mai guba da aka yi a Abidjan

Halin da ake ciki dangane da zaman lafiyar Uganda na daga cikin muhimman batutuwan Afurka da suka samu shiga kanun rahotannin Jaridun Jamus a wannan makon. A nata bangaren jaridar DER TAGESSPIEGEL ‘yar Berlin cewa tayi:

“Tun da ake a cikin shekaru 20 da suka wuce arewacin Uganda bata taba samun haske a game da makomar zaman lafiyarta ba kamar a wannan karon. Domin kuwa tuni daruruwan dakarun kungiyar tawaye ta LRA suka taru a wuraren da aka tanadar musu a kudancin Sudan a karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar da ake tattaunawa kanta a halin yanzu. A baya ga haka akwai wasu dakarun kungiyar da suka fito daga mabuyarsu a gabacin Kongo da arewacin Ugandan da kudancin Sudan. Gwamnatin shugaba Museveni ta kara wa’adin da ta kayyade wa dakarun domin yin hakan a fafutukar kawo karshen yakin basasar yankin arewacin Udangan da yayi sanadiyyar rayukan dubban mutane a cikin shekaru ashirin da suka wuce.”

A karo na farko sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya fito fili yana mai barazana akan wata kasa dake da wakilci a majalisar kamar yadda jaridar DIE ZEIT ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

“Sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya fito karara yana mai gargadi ga kasar Sudan a game da in har ta ki amincewa da tsugunar da dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar a Darfur domin dakatar da ta’asar kashe-kashe na gilla dake wanzuwa a yankin to kuwa za’a dauki matakai na ladabtar da shuagabannin kasar, wadanda su ne ummal’aba’isin wannan masifa. Wato dai a takaice in har shuagabannin na Sudan ba su amince da tsugunar da dakarun kiyaye zaman lafiya na MDDr ba za a daukaka kara kansu a kotun kasa da kasa akan miyagun laifuka na yaki dake garin The Hague.”

Ita kuwa Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta mayar da hankalinta ne akan tabargazar dattin masana’antun nan mai guba da aka jibge a wasu yankuna na birnin Abidjan a kasar Cote d’Ivoire. Jaridar tayi nuni da cewar:

“Duk da ikirarin da kamfanin Trafigura Beheer na kasar Netherlands ke yi na cewar tana da cikakkun takardun dake ba ta damar fitar da dattin zuwa Cote d’Ivoire, amma wannan ba kome ba ne illa tsabar karya. Domin kuwa akwai yarjeniyoyi da kudurori na kasa da kasa dake haramta fitar da irin wannan datti mai guba zuwa kasashen Afurka. Amma ire-iren wadannan abubuwan su kan faru a kasashen da ba a da wata tsayayyar gwamnati, kuma wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin kamfanin na Netherlands da wasu jami’an siyasa ‘yan cin-hanci a kasar Cote d’Ivoire.”