1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan mutane sun rasu sakamakon fashewar bututun mai a Nijeriya

December 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuWR

Wani bututun mai da ya fashe a birnin Legas a tarayyar Nijeriya ya halaka mutane da dama yayin da wsu suka samu kuna iri dabam-dabam. Wannan hadarin ya faru ne a Agbule Egba darewacin birnin na Legas. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya rawaito sakatare janar na kungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya Abiodun Orebiyi na fadin cewa akwai yiwuwar mutane fiye da 300 suka rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin kwasar mai yayin da bututun ya fashe kuma ya kama da wuta.Orebiyi ya nunar da cewa:

“An kashe wutar kuma muna iya ganin karin gawawwaki da suka kone. Yanzu dai muna kokarin gane ainihin yawan daruruwan mutane da suka mutu ne sakamakon fashewar bututun wanda ya auku da misali karfe daya na dare. Bata gari suka fasa bututun don satar mai.”